An yi garkuwa da iyayen Shugaban Majalisar Zamfara | Aminiya

An yi garkuwa da iyayen Shugaban Majalisar Zamfara

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Sagir Kano Saleh

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matar mahaifain Shugaban Majalisar da kawunsa da kuma wasu mutum hudu.

Maharan sun yi garkuwa da su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin nasu, Magarya, da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara mai wakilatar mazabar Zurmi ta Yamma, Salihu Zurmi, ya ce harin da ’yan bindiga suka kai a yammacin ranar Laraba, “Shi ne karo na hudu da aka kawo hari garin.

“Na farko an kashe wasu mutane, a na biyu kuma suka banka wa wasu gidaje wuta sannan suka kwashe shannu da sauran dabbobin da ake kiwo,” inji sh.

Darakata-Janar kan Yada Labaran Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Mustapha Jafaru Kaura, ya shaida mana cewa za su fitar da sanarwa a game da lamarin.

“A yanzu haka ina tare da Shugaban Majalisar, ku dan ba mu lokaci, za mu fitar da sanarwa,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

Shi ma da aka tuntube shi, kakakin ’yan sanda a Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce Rundunar za ta fitar da sanarwa.

A kwanakin baya, ’yan bindiga sun kashe Shugaban Kwamitin Kudi an Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, a kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Jihar.

Kwanaki kadan bayan nan, wasu ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocin gwamnan Jihar Kano hari a kan hanyar Gusau zuwa Kano.

’Yan bindiga sun tsananta kai hare-haren a Jihar Zamfara, inda a kwanakin baya suka harbo wani jirgin soji a tsakanin Jihar da makwambciyarta, Jihar Kaduna.

Mun kuma kawo muku labari inda Sanata Sa’idu Dansadau, ya yi zargin cewa ’yan bindiga sun addabi mazabarsa da hare-hare, saboda ba su ji dadin tube Sarkin Dansadau da Gwamnatin Jihar ta yi, bayan samun shi da laifin alaka da ’yan bindiga.

SAURARI: Abin da ke kawo yawan mutuwar aure a kasar Hausa: