✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An yi garkuwa’ da mutane a masallaci a Delta

Maharan sun sace limami sannan suka harbi mutum 11 a lokacin da ake Masallacin Juma’a na garin Ughelli

’Yan bindiga sun kutsa wani masallacin Juma’a tare da yin awon gaba da kimanin mutum uku a ranar Juma’a a Jihar Delta.

Wata majiya ta ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da Na’ibin Limamin Babban Masallacin Juma’a na garin Ughelli, Malam Muhammadu Sani, wanda ke jagorantar Sallar Asuba a a lokacin da aka kai harin.

Kakakin Kungiyar Al’ummar Arewa a Ughelli ta Arewa, Ahmad Garba, ya ce, “Da misalin karfe 6 na Asuba  mutum biyu daga cikin ’yan  suka shiga cikin masallacin suka yi awon gaba da Mallam Muhammadu Sani, kafin su fita daga masallacin sai da suka harbi mutum 11.”

Wani wanda dattijo mai shekara 63 daga cikin wadanda ’yan bindigar suka harba, Muhammad Bagudu, ya shaida mana a gadon asibiti cewa, maharan, “Sun harbe ni da dan uwana da daya daga cikin limamanmu, sannan suka tafi da Malam Muhammadu Sani.”

Wani ganau kuma makwabcin masallacin, mai suna Larry, ya ce karar harbe-harben maharan ne ya tashe su, “ana tsaka da haka kuma muka rika jin kururuwar mutanen dake cikin Masallacin suna neman agaji.”

Kakakin ’yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da harin, amma ya ce mutum 11 ne aka jikkata.

Edafe bai ce uffan game da batun garkuwa da mutane a masallacin ba, amma ya ce, “’yan sanda sun fara gudanar da bincike domin kamo maharan kuma nan gaba za mu sanar da ku.

“Amma kawo yanzu babu wanda ka kama kan lamarin, amma ina tabbatar muku cewa masu laifin za su shiga hannu.”