✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mutum 46 a sabon hari a Kaduna

Maharan sun dauki kusan minti 10 zuwa 20 suna cin karensu babu babbaka.

Akalla mutum 46 ne suka fada tarkon masu garkuwa da mutane a garin Agunu Dutse da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Da yake zantawa da Aminiya, Galidiman Agunu Dutse, Maurice Clement Tanko, ya ce maharan sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 12.30 na ranar Alhamis.
“Da misalin karfe 12.30 ne wadansu yan sa-kai suka lura da wani motsi wanda ba a saba gani ba a wani yanki na wajen garin da ke da tazarar mita 200.
“Sun rika haske-haske da fitilu da kuma neman jin ba’asi amma babu wanda ya tanka musu.
“Maharan sun dauki kusan minti 10 zuwa 20 suna cin karensu babu babbaka, amma sai suka lura yan sa kai din na neman cim masu,” a cewar Galidiman.
Ya kara da cewa akwai wani mutum daya mai suna Abubakar Sule da ya jikkata a yayin harin, amma a halin yanzu yana samun kulawa a wani asibiti.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige bai ce komai a kan lamarin ba.