✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da tsohon Manajan gidan Talabijin na Katsina

An yi awon gaba da shi tare da ’yarsa mai shekara 15.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Manajan Gidan Talabijin na Jihar Katsina, Ahmed Abdulkadir, ta re da wata ’yarsa mai shekara 15 a gidansa da ke cikin garin Bakori, Jihar Katsina.

Iyalanshi sun sanar ta shafinsa na Facebook cewa ’yan bindigar sun afka gidan ne suka yi awon gaba da shi tare da ’yar tasa Laila a ranar Litinin.

Ahmed Abdulkadir ya yi manajan Gidan Talabajin na Jihar Katsina a wajen shekara ta 2004, daga bisani ya koma Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC).

Wakilinmu ya ruwaito cewa a baya-bayan nan ayyukan masu garkuwa da mutane a Jihar Katsain sun karkata zuwa yankunan hananan hukumomin Bakori da Funtuwa da kuma Kafur, inda a cikin kwana uku sun yi awon gaba da mutum kusan 7.

Hakan kuma na zuwa ne kasa da mako guda bayan Gwamnatin Jihar Katsina ta rufe wasu hanyar Jibiya, ta karkatar da matafiya zuwa hanyar Funtuwa, saboda matsalar ayyukan ’yan bindiga.

Dokar ta kuma rufe kasuwannin dabbobi 14 tare da hana jigilar dabbobin a manyan motoci ko dakon ice a fadin jihar.

Ta kuma haramta sayar da fetur a jargoki tare da kayyade adadin fetur din da gidajen mai za su sayar wa mutum guda, kar ya wuce na N5,000.

Sannan ta jaddada haramcin zirga-zirgar kowadanne irin babura daga karfe 6 na safe zuwa karfe 10 na dare a garin Katsina, a sauran wurare kuma zuwa karfe 6 na yamma.

Ta kuma kayyade wa babura masu kafa uku daukar mutum uku kacal, masu kafa biyu kuma mutum biyu.

Sai dai kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu an samu hare-hare da garkuwa da mutane, ciki har da wani dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina da iyalan wani dan majalisar.