✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da ’yan mata da matan aure a Kaduna

Mutum akalla 11 aka yi garkuwa da su a garin Birnin Yero.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da ’yan mata da matan aure akalla biyar a garin Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Igabi da Jihar Kaduna.

A cikin dare ne dai maharan suka far wa garin suka yi awon gaba da mutum bakwai, amma daga bisani biyu daga cikin mutanen suka samu suka tsere.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar wa wakilinmu cewa matan aure da ’yan mata ne aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kafin wayewar garin Laraba.

Ya ce awon gaba da matan da aka yi mako guda bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum shida a garin ya jefa mazauna cikin tashin hankali.

Shi ma wani mazaunin garin ya ce an yi garkuwa da wasu mutane a garin a ’yan kwanakin baya, ko da yake ba mu iya tantance zargin nasa ba.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya ce ba su samu labarin harin ba a hukumance.

Harin na Birnin Yero an kai shi ne ’yan sa’o’i bayan ’yan bindiga sun kutsua unugwar Keke II da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutum 18.