✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da yaro mai wata 8 a Zamfara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mace mai shayarwa da danta mai wata takwas.

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da karamin yaro mai wata takwas da mahaifiyarsa a unguwar Damba da ke garin Gusau na Jihar Zamfara.

Da sanyin safiyar Laraba ne masu garkuwa da mutane suka kutsa gidan suka wani dan siyasa a unguwar suna ta harbin kofofin dakunan gidan bayan ya ki bude musu su shigo.

Shigansu cikin gidan ke da wuya suka harbi dan siyasan sannan suka tafi da matar da dan da take shayarwa mai wata takwas a duniya.

“Sun razana mutane da harbi bayan shigansu gidan da misalin 1 na dare.

“Shi kuma sun harbe shi a hannu sannan suka yi wa tagogi da kofofin dakunan gidan ruwan harsasai.

“An kai shi asibiti saboda jinin da ya yi ta zubarwa, mutane na tururuwa zuwa gidan domin jajanta wa iyalan,” inji wani dan unguwar.

kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwan lamarin.

Ya ce Babangida Ibrahim, tsohon kansilan Damba shi ne wanda aka kai harin gidansa aka yi awon gaba da matarsa mai shayarwa da danta.

“Rundunarmu na bin sawun masu garkuwar domin ceto wadanda aka sace.

“Kwamishinan ’yan sandan Jihar Zamfara, Hussaini Rabi’u, ya ba da umarni a gudanar da cikakken bincike kan lamarin a kuma tabbata an kamo bata-garin,’’ inji Shehu.