✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi gobara a ofishin INEC a Zamfara

INEC ta ce ba a samu asarar rai ko daya ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa gobara ta tashi a ofishinta da ke Karamar Hukumar Kauran Namoda a Jihar Zamfara.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa Festus Okoye ne ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja, yana mai cewa kwamishinan zaben Jihar Zamfara, Farfesa Sa’idu Babura Ahmed ne ya bayyana faruwar lamarin ga hukumar.

Okoye ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 11:00 na daren ranar Litinin 2 ga Mayu, 2022.

Sai dai ya ce ba a samu asarar rai da muhimman kayayyaki kamar katin zabe da na’urorin rajista ba sakamakon aka ajiye su cikin akwatunan da ke hana kamawa da wuta.

“Duk da haka ginin ya lalace sosai. Wasu kafofi da kayan aikin ofishin sun lalace.

Sai dai hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara da wasu matasa sun yi kokarin shawo kan gobarar.

“Tuni ‘yan sanda da hukumar kashe gobarar jihar suka fara bincike don gano musabbabin tashin gobarar don bai wa INEC shawara kan daukar matakin da ya dace,” in ji Okoye.