Daily Trust Aminiya - An yi gunduwa-gunduwa da gawar matashiya

An yi gunduwa-gunduwa da gawar matashiya

An kashe wata matashiyar mata tare da yi wa gawarta gunduwa-gunduwa sannan aka jefar.

Shaidu sun ce an tsinci gawar matar an yanke mata al’aura da nonuwanta da wasu sassan jikinta.

“Binciken likitoci ya gano cewa mutanen da suka kashe ta sun yanke farjinta da nonuwanta, shi ya sa ake zargin matsafa ne”, inji kakakin Hukumar Tsaro ta ‘Civil Defence’ reshen Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi.

Ya ce: “Ranar Alhamis 10 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 12:30 na rana ne matsafa suka kashe Hassana Mohammed, ’yar gidan Yarugaba, a Kaiama, suka jefar da gawarta a titin Kanikoko da ke garin.”

Afolabi ya ce ana ci gaba da gudanar a bincike domin gano wadanda suka kashe marigayiya Hassana, su fuskanci hukunci.

Kisan gillar da aka yi wa matashiyar ya jefa mazauna unguwar  ta Kanikoko da ke Karamar Hukumar  ta Kaiama cikin tashin hankali.

Tun da farko, ’yan uwan matashiyar suka sanar da bacewarta.

Bayan neman ta ba tare da an dace ba ne iyalan matashiyar suka sanar da jami’an tsaro da ’yan banga, wadanda daga baya suka gano gawarta a cikin wannan mummunan yanayi.

A ranar Juma’a aka yi mata jana’iza, aka kuma binne gawar da aka yi wa gunduwa-gunduwa.

Karin Labarai