✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi gwajin sabon irinn wake a Kano

A karshen makon da ya gabata ne aka kaddamar da gwajin shukar wani sabon irin wake a garin Tudun Wada da ke Jihar Kano don…

A karshen makon da ya gabata ne aka kaddamar da gwajin shukar wani sabon irin wake a garin Tudun Wada da ke Jihar Kano don rage wa manoma irin asarar da suke yi.

Cibiyar Binciken Ayyukan Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello ce ta samar da sabon irin waken.

Da yake jawabi a bikin, Shugaban Cibiyar Farfesa Muhammad Isyaku ya bayyana cewa sabon irin waken mai lakabin ‘Maruka’ ba ya illa sannan ba ya janyo matsala ga muhalli.

Shugaban wanda Mataimakiyar Daraktan Cibiyar Farfesa Aisha Abubakar ta wakilta ya yi kira ga manoman da su rungumi sabon irin domin zai taimaka musu wajen samun yabanya mai kyau.

“Wake ne da bai bukatar kashe kudi domin ba ya bukatar feshi da yawa. Feshi biyu ma ya ishe shi. Kun ga manomi ya sami sauki domin idan a da yana sayen lita 10 na feshi yandu bai fi ya yi amfani da lita biyu ba. Kun ga manomi ya sami canjinsa a aljihu don haka manoma su yi kokari su sami irin nan don zai sa su sami alheri sosai”, inji shi.

Shi ma da yake jawabi jagoran wadanda suka gudanar da aikin kirkirar irin, Dokta Muhammad Lawan Umar, ya bayyana irin matakan da suka bi wajen samun nasarar samar da irin wanda ke bijirewa tsutsotsin maruka.

“Wake ne da aka samar da shi ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma aiki tukuru daga masana masu bincike na duniya wajen samar da shi. Akwai wasu daga kasar Austireliya da Najeriya da kuma wasu kasashe na Afrika.”

Malam Khalid Umar Salihu yana daya daga cikin manoman da aka yi gwajin shukar waken a gonakinsu ya bayyana cewa akwai bambanci tsakani irin da suka saba amfani da shi da kuma wannan sabon, ‘’kamar yadda na fahimta wannan iri ne da zai sa mu sami sauki kwarai da gaske. Domin ba ya daukar tsawon lokaci wajen fitowa. Mun yi murna kwarai da hakan.”

Shi ma a jawabinsa Hakimin Tudun Wada Alhaji Muhammad Ibrahim Dankadai wanda wakilinsa Alhaji Kabir Alassan Yaryasa ya wakilta kira ya yi ga ci gaba da ta samar da sabon irin da yawa domin biyan bukatun manoman yankin.