✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An Yi Gwanjon Kayan ’Yan Wasan Netherlands Don Taimaka Wa Ma’aikata Baki A Qatar

Wani gwanjon rigunan ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands da aka yi ranar Litinin don tallafawa ’yan gudun hijira, ya samar da Dalar…

Wani gwanjon rigunan ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands da aka yi ranar Litinin don tallafawa ’yan gudun hijira, ya samar da Dalar Amurka 402,934.

Kamanin Dillancin  Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa kasar za ta yi amfani da kudaden ne wajen taimaka wa ma’aikatan ’yan gudun hijira da ke Qatar.

Hukumar kwallon kafa ta kasar tq ce tana shirin yin aiki tare da Kungiyar Kwadago ta Duniya, don amfani da kudaden  wajen kare hakkoki, da ba da taimakon shari’a, hadi da cigaban ma’aikatan da zamantakewarsu, musamman a harkoki irinsu kwallon kafa.