✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi gwanjon rigar kwallon Maradona kan Naira biliyan 3.6

Rigar ta kafa tarihi sau biyu wajen zama mafi tsada a fagen gwanjon kayayyaki irin wannan.

An sayar da rigar da shahararren dan kwallon kafa marigayi Diego Maradona, ya yi amfani da ita yayin karawar Argentina da Ingila a gasar cin Kofin Duniya a shekarar 1986 kan Fam miliyan 7.1 daidai da Naira biliyan 3.6.

Rigar marigayin ita ce ta zama mafi tsada a gwanjon kayayyakin wasanni motsa jiki na tuna baya wanda gidan gwanjo na Sotheby ya yi a ranar Laraba.

Maragayi Maradona ya yi amfani da wannan riga ne bayan hutun rabin lokaci a wasan kusa da karshe da aka buga tsakanin Argentina da Ingila inda Agentina ta samu nasarar doke abokiyar karawarta.

Sotheby ya yi kiyasin farashin rigar tsakanin Fam miliyan 4 zuwa Fam miliyan 6, wanda kafin wannan lokaci rigar na hannun abokin hamayyar Maradona na 1986, wato Steve Hodge.

Rigar Maradona din mai ruwan shudi, ta kafa tarihi sau biyu wajen zama mafi tsada a fagen gwanjon kayayyaki irin wannan.

Da wannan rigar ta zama kan gaba wajen daraja fiye da ta zakaran ‘baseball’, Babe Ruth wadda aka biya farashi mafi tsada a kanta a 2019.

Har ila yau, rigar ce mafi tsadar abubuwan tuna baya a wasanni kowane iri, matsayin da a baya littafin Pierre de Coubertin na gasar Olympics ke rike da shi tun a shekarar 1892.

Maradona na sanye da wannan riga ce a lokacin da ya ci kwallaye biyu masu muhimmanci yayin wasansu da Ingila a gasar cin kofin duniya, wadanda aka yi wa lakabi da ‘Hand of God’ da kuma ‘Goal of the Century’.