✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar kanin Dahiru Mangal

An gudanar da Sallar Jana'izar Alhaji Bishir, kanin fitaccen dan kasuwa Alhaji Dahiru Bara'u Mangal a Katsina bayan kawo gawarsa daga Abuja

An gudanar da Sallar Jana’izar Alhaji Bishir, kanin fitaccen dan kasuwa Alhaji Dahiru Bara’u Mangal a Katsina bayan kawo gawarsa daga Abuja inda Allah Ya karbi rayuwarsa a wani asibiti.

Alhaji Bishir cikinsu daya da Alhaji Dahiru kuma shi ne wanda yake kula da harkokin Kamfanin iragen Max Air a babban ofishinsu da ke Kano.

Mutuwarsa dan uwa shakiki da ya rage wa Alhaji Dahiru Mangal, ita ce ta uku ta shakikan attajirin a wannan shekara ta 2022.

Shi dai Alhaji Bishir cikinsu daya da Alhaji Dahiru kuma shi ne wanda yake kula da harkokin Kamfanin iragen Max Air a babban ofishinsu da ke Kano.

Kafin samuwar kamfanin Max Air, ya taba zama jami’in hidimar masu zuwa aikin Umra a karkashin kamfanin jigilar masu zuwa Umra na Masanawa Travelling Agency.

Daga baya a shekarar 2007 Dahiru Mangal ya kawo kamfanin Max Air bayan wata matsala da ta haddasa rashin daukar Alhazan Jahar Katsina a 2006 lokacin Marigayi Umaru ‘Yar’ Aduwa yana Gwamnan Jihar Katsina.