An yi jana’izar Mama Taraba | Aminiya

An yi jana’izar Mama Taraba

Babban Limamin Muri, Imam Nuru Dinga ya jagoranci jana’izar. (Hoto: Magaji IsaHunkuyi).
Babban Limamin Muri, Imam Nuru Dinga ya jagoranci jana’izar. (Hoto: Magaji IsaHunkuyi).
    Magaji Isa Hunkuyi, Jalingo da Sagir Kano Saleh

An gudanar da jana’izar tsohuwar Ministar Harkokin Mata ta Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, wadda Allah Ya yi wa rasuwa a makon jiya.

Sallar Jana’izar Aisha Alhassan wadda aka fi sani da Mama Taraba, ta gudana ne a Fadar Sarkin Muri,  Jihar Taraba, da Magariba, ranar Litinin.

Gawar marigayiyar ta iso Filin Jirgin Sama na Jalingo ne aka yi mata sallar jana’izar, wadda Babban Limamin Muri, Imam Nuru Dinga ya jagoranta.

Dubun dubatar mutane ne suka halarci sallar jana’izar, kafin a kai ta makwancinta a Makabartar Jeka da Fari.

Mahalarta daga ciki da wajen Jihar Taraba sun hada da Mataimakin Gwamnan jihar, Haruna, sarakuna da hakimai, da ’yan majalisar jiha da ta tarayya tsoffi da masu ci.

Tun bayan rasuwarta ake ta aikewa da sakonnin ta’aziyya ga Gwamnati da al’ummar Jihar Taraba da iyalan mamaciyar.

Marigayiya Jummai Alhassan, fitacciyar ’yar siyasa ce da ta yi takarar Gwamnan Jihar Taraba a 2015, amma tasha kaye a hannun Gwamna mai ci, Darius Ishaku.

Tsohuwar mata ce ga Farfesa Ango Abdullahi wanda ta haifa wa ’ya’ya uku, kuma ta rasu ta bar mahaifinta da ’ya’ya uku da kuma jikoki 13.