✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi kutse a shafukan Shugaban Jami’ar Bayero

Ya ankarar da jama'a cewa masu kutsen suna damfarar jama'a ne ta hanyar amfani da shafukan sada zumuntarsa na bogi

Masu damfara da intanet sun yi kutse a a layin waya da shafukan sada zumuntan Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas.

Farfesa Sagir da kansa ne ya sanar da haka, yana mai ankarar da jama’a cewa masu kutsen suna damfarar jama’a ne ta hanyar amfani da shafukan sada zumuntarsa da suka yi kwafinsu.

“Masu damfara ta intanet din sun yi kwafin shafukan zumuntana na bogi a Instagram da Facebook da WhatsApp da Messenger da LinkedIn,” wadanda suk amfani da su wajen damfarar al’umma.

Ya ci gaba da cewa, “A taikaice sun yi nasarar damfarar wadansu daga cikin mutanen da na sani.

“Lambobin wayar da suke amfani da su wajen yin damfarar su ne: +2349161843081; +2349162511721; +2349162511622.”

Don haka Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani wanda ya kira su ta waya ko ta kafofin sada zumunta ya nemi su ba shi wani da sunansa.

“Don Allah ina rokon ku da cewa ku yi watsi da wadannan ’yan damfara, saboda kutse suka yi a layin wayata domin aikata wannan mummunar sana’a, kuma wani mai suna Dokta Olabanji, ne ke yin wannan kazamar sana’a.