✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi sallar neman saukin harin ’yan bindiga a Zariya

An yi addu’o’in neman Allah Ya kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a Zariya.

A sakamakon yawiatar hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane da suka tsorata jama’a a sassan Zariya, malaman Musulunci sun gudanar da salloli da addu’o’in neman Allah Ya kawo karshen lamarin.

Daruruwan al’ummar Musulmi ne suka halarci sallar a ranar Laraba, domin rokon Allah Ya kawar da fitinar daga Karamar Hukumar ta Zariya.

Daya daga cikin wadanda suka shirya addu’o’in, Malam Tanimu Abubakar Mai Rawani, ya ce Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW), a duk lokacin da wani abu ya buwayi mutane, su kaskantar da kai su koma bayan gari domin addu’o’i da neman Allah Ya kawo musu dauki.

Malam Tanimu ya kara da cewa al’ummar Zariya na cikin tsaka mai wuya kuma ba su iya barci ido rufe saboda matsalar tsaron na neman fin karfin gwamnati.

A cewarsa, suna sa ran da addu’o’in, cikin yardar Allah batun ayyukan ta’adanci ya zo karshe a Najeriya.

Da yake jawabi bayan kammala addu’o’in, Sheikh Habibu Usman ya ce: “Ta’adanci irin na masu garkuwa da mutane ba shi da alaka da addini gaba daya kuma ya saba da koyarwar Musulunci.

“Don haka wajibi ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wurin kawo karshen wannan matsala.’’

Wani Basarake a Masarautar Zazzau, Garkuwan Makarantar Zazzau, Alhaji Shamsuddin Aliyu, ya ce lokaci ya yi da za a bar kowa ya dauki matakin kare kanshi, saboda a zahiri gwamnati ta gaza.

Ya ce dole jama’a su koma ga Allah kowa ya gyara zuciyarsa, abin da ya ce ake sa ran idan aka yi za a samu mafita.

Basaraken ya kara da cewa jarrabawa iri biyu jama’a ke fama da su: akwai na gwamnati da kuma na masu garkuwa da mutane.

Ya ce korar ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi ba gaira ba dalili yana sabbaba karuwar marasa aikin yi.

Ya bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai su samar wa da matasa aikin yi domin rage zaman kashe wando da ake fama da shi yanzu haka.