✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi sulhu tsakanin Alhassan Doguwa da Murtala Garo

Da ni da Murtala Sule Garo mun yafi juna kan abubuwan da suka faru.

An dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, da dan takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci zaman sulhun wanda aka gudanar a gidan Gwamnati.

Shugaban APCn ya ce a yanzu komai ya daidaita a jam’iyyar, babu sauran wata rigima.

“Yanzu ina tabbatar wa jama’a cewa babu wata matsala a Jam’iyyarmu. An yi sulhu tsakanin Alhassan Ado da Alhaji Murtala Garo. Sun yafe wa juna. Komai ya wuce. Mun zama uwa daya uba daya.”

Abdullahi Abbas ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da zama da juna lafiya domin kai jam’iyyar ga nasara.

A nasa jawabin, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Tarayya, Ado Doguwa, ya tababatar da batun sulhun inda ya ce shi da Murtala Sule Garo sun yafi juna kan abubuwan da suka faru.

“Tun karfe 11:00 na dare muke zaune har zuwa Asubahi akan wannan matsala, kuma Alhamdulillah mun yafe wa junanmu.

Idan za a iya tunawa a makon jiya ne aka sami sabani tsakanin Alhasasan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo, a lokacin da wasu shugabannin jam’iyyar ke tattaunawa a gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, inda suka yi musayar yawu, har Doguwa ya jefi Garo da kofin shafi a baki.