✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Adam A. Zango haihuwa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya samu karuwar ‘ya mace. Na hannun damansa, Mansur Make-Up, ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa maidakin…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya samu karuwar ‘ya mace.

Na hannun damansa, Mansur Make-Up, ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa maidakin jarumin, Safiya Umar Chalawa, ta haihu.

A shafin nasa ya sanya hoton jarumin da matar tasa sannan ya rubuta cewa, “Allah Ya raya mana a kan Sunnah”.

Idan ba a manta ba, a watan Afrilun shekarar 2019 ne aka sha bikin jarumin da matarsa Safiya.