✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa bankuna 3 fashi a rana guda a Kogi

Bayan gamawa da bankuna uku, ’yan fashi sun rika bin masu harkar POS suna kwace musu kudade

’Yan fashi dauke da manyan makamai sun kutsa cikin bankuna uku da tsakar rana tare da yin awon gaba da kudaden da ba a tantance yawansu ba a Jihar Kogi.

A ranar Talata ’yan fashi a motoci da babura suka kutsa cikin rassan bankunan Zenith da UBA da kuma First Bank a garin Ankpa da ke jihar da misalin karfe 2 na rana.

Bayan fashin, “Sun zaburi ababen yawansu suka bi ta Titin Okpo, amma babu wanda ya iya fitowa saboda yadda suke ta harbi kan mai uwa da wabi,” in ji wani ganau.

Shaidu sun ce ’yan fashin sun fara shiga bankin UBA ne, daga nan suka kutsa Zenith sannan suka shiga FirstBank.

Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa bayan maharan sun yi wa bankunan fashi; sun shafe kusan awa guda suna bin masu harkar cirar kudi na POS da ke kusa da bankunan suna yi musu fashi kafin su wuce suna harbe-harbe.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto babu tabbacin ko akwai wanda ya rasa ransa a harin.

Amma wani mazaunin garin na Ankpa, Ahmed, ya ce, “Ba abin mamaki ba ne idan aka samu asarar rai.”

Wani dan garin ya ce bayan tafiyar ’yan fashin, an ayarin rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro sun nufi yankin da abin ya faru.

Har aka kammala hada wannan rahoto dai Kakakin ’yan sanda na Jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa rubutaccen sako da muka tura masa na neman karin bayani ba.