✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Buhari rigakafin Coronavirus zagaye na biyu

A watan Maris ne Shugaba Buhari ya karbi zagayen farko na allurar.

A yau Asabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi zagaye na biyu na allurar rigakafin cutar Coronavirus.

An yi wa shugaban allurar rigakafin ta kamfanin AstraZeneca a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja kamar yadda hadiminsa na kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kazalika, Fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa wasu hotunan Shugaban yayin da yake karbar rigakafin, inda ya nuna shaidarsa domin sauran al’ummar kasar su yi koyi da hakan.

Shaidar da Shugaban ya haska na dauke da sakon tabbatar da inganci da kuma aminci a kan allurar rigakafin.

Ana iya tuna cewa, a farkon watan Maris ne Shugaba Buhari ya karbi zagayen farko na allurar, inda a yanzu ya kammala karbar rigakafin cutar kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.

Lokacin da Buhari yake haska shaidar karbar rigakafin
Lokacin da jami’an lafiya ke yi wa Buhari allurar rigakafin