✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa ma’aikata karin albashi a Anambra

Gwamnan ya yi wa ma'aikata kyautar dubu 15 don yin bikin Kirsimeti.

Gwamnan Anambra, Charles Soludo, ya yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar karin kashi 10 na albashi, wanda zai fara aiki a watan Janairun 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ma’aikatan gwamnati na 2022 a dakin taro na Jerome Udoji da ke Awka.

Kazalika, Soludo ya ba da umarnin bai wa ma’aikatan kyautar N15,000 don gudanar bikin Kirsimeti a jihar.

Ya sake jadadda aniyarsa na ci gaba da yakar bata gari a lungu da sako ja jihar.

Anambra dai na fama da hare-haren ’yan awaren Biyafara (IPOB), wadanda sukan sanya dokar zaman gida.

Amma gwamnan ya ce zai ci gaba da yaki da IPOB har ya kawo karshensu.