✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa sama da fursunoni 800 afuwa a Myanmar

Shugaban gwamnatin soji, Min Aung Hlaing ya ba da wannan umarni na sakin fursunoni 814.

Gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta sanar da yi wa fursunoni sama da 800 afuwa, a yayin da ta gudanar da faretin nuna kwanji a babban birnin kasar don bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai shekaru 75 da suka wuce.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa a ranar Asabar ce shugaban gwamnatin soji Min Aung Hlaing ya ba da wannan umarni na sakin fursunoni 814, abin da aka saba yi a rana irin wannan.

Kasar ta fada cikin rikici tun a shekarar da ta gabata bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya haddasa zanga zanga da ta yi sanadin mutuwar sama da farar hula 1,500.

Ana bikin an shekara shekara ne don tunawa da ranar da jagoran gwagwarmayar neman yancin kai, Aung San da kabilu da dama  suka  shiga yarjejeniyar yanto Burma daga mulkin mallakar Birtaniya.

A bara ce Janar Min Aung Hlaing ya sanar da cewa za a yi wa fursunoni 5000 saboda dalilai na jin kai biyo bayan dubban mutanen da aka kama saboda zangar-zangar adawa da juyin mulkin da aka yi a watan Fabrairun shekarar da ta gabata.