✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Sarkin Karaye rigakafin Coronavirus

Da safiyar Lahadi aka yi wa Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar II allurar rigakafin cutar Coronavirus a fadarsa da ke garin Karaye a jihar Kano.…

Da safiyar Lahadi aka yi wa Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar II allurar rigakafin cutar Coronavirus a fadarsa da ke garin Karaye a jihar Kano.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun fadar, Haruna Gunduwawa.

Gunduwawa ya ce ma’aikatan lafiya ne suka yi wa Sarkin rigakafin tare da dukkan iyalansa da kuma sauran hadiman da ke fadar.

Da yake jawabi bayan karbar rigakafin, Sarkin ya ja hankalin al’umma a kan su tabbatar an musu rigakafin domin rubanya fafutikar da ake yi ta yaki da annobar Coronavirus.

Sarkin ya kuma bayyana amincinsa a kan allurar a yayin da wani sashe na duniya ke bayyana fargaba gami da juya baya a kanta.