✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Shugaban APC kisan gilla a Sakkwato

A yayin farmakin, ’yan bindigar sun harbe dan uwan dan siyasar da ya kai masa dauki

Wasu ’yan ina-da-kisa sun yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Mazabar Asara a Karamar Hukumar Gwadabawa ta Jihar Sakkwato, Alhaji Iliya Agajiba, kisan gilla.

A yayin farmakin, ’yan bindigar sun harbe dan uwan shugaban jam’iyyar, wanda ya kai masa dauki.

Sun kuma yi awon gaba da dabobbin dan siyasar da na sauran al’ummar yankin.

Wani mazaunin Asara da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce maharan da yawansu ya kai 15 sun yi wa yankin dirar mikiya ne a cikin dare ranar Asabar.

Wasu mazauna yankin na zargin kisan dan siyasar da dan uwansa na da nasaba da siyasa, wasu kuma ke ganin sa a matsayin harin ’yan bindiga.

Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

Kazalika, jin ta bakin kakakin rundunar, DSP Sunusi Abubakar, ya ci tura.

Karamar Hukumar Gwadabawa na daga cikin yankunan da ke fuskantar kazaman hare-haren ’yan bindiga a yankin Gabashin Jihar Sakkwato.