✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa tsofaffi kisan gilla kan zargin maita

Jama'ar gari sun yi ta saran tsofaffin da makamai har sai da suka rasu.

Jama’ar gari sun gana wa wasu tsofaffi biyu azaba har sai da suka mutu saboda zargin maita a Jihar Binuwai.

Matasan garin Mbaaku Mbasombo sun yi wa tsofaffin dirar mikiya suka lakada musu duka sannan suka daure su, suna jan su da igiya a kan titi, har sai da suka ce ga garinku nan.

Wani dan garin da ke Karamar Hukumar Gwer ta Gabas, ya ce, Matasan “Sun rika saran tsofaffin da adduna da gatari.

“Har daura musu igiya a wuya suka yi, suka rika jan su a kan titi sai da suka mutu.

“Tsofaffin sun yi ta kururuwar neman agaji tare da nesanta kansu da zargin da ake musu na maita, amma matasan ba su raga musu ba”.

Dattawan masu suna Kwaghange Ugbu da Atuur Shaaja, sun gamu da wannan kisan gilla ne bayan rasuwar wani matashi daga cikin danginsu, wanda ya kammala karatun sakandare.

Wani dan garin ya ce saurayin mai suna David Terseer Nongobo ya yanke jiki ya fadi ne a yayin da yake tsaka da aiki a gona, aka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar cewa ya rasu.

Da jin haka, sai matasan garin suka yi dirar takakkiya a gidan dattawan bisa zargin su da kashe yaron ta hanyar maita.

Ganau din ya ce, “Iyalai da dangin wadannan dattawa da aka yi wa wannan aika-aika sun yi kokarin kawo musu dauki, ganin irin cin mutuncin da ake musu, amma matasan suka danne su.

“Bayan rasuwar tsofaffin kuma matasan sun hana kowa taba gawarwakin, sai washegari aka dauke su zuwa dakin ajiyar gawa.”

Kakakin ’yan sanda a Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta tabbaar da faruwar lamarin, sannan ta ce matasan da ake zargi sun tsere, amma ana neman su.

A baya-bayan nan, an samu karuwar irin wannan kisan gilla da sunan zargin maita a Jihar Binuwai, inda ko a kwanaki baya an samu irin haka a yankin Shangev Tiev da ke Karamar Hukumar Konshisha ta jihar.