✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi yunkurin caka wa Shugaban Mali wuka a filin Idi

Maharin ya yi yunkurin hallaka Shugaban ne da wuka amma bai yi nasara ba.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, Assimi Goita ya tsallake rijiya da baya sakamakon yunkurin caka masa wuka da aka yi a babban filin Idi na babban birnin kasar, Bamako, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

“Jami’an tsaro sun sami galaba cikin gaggawa akan maharin. Yanzu haka an fara bincike a kai,” inji Fadar Shugaban Kasar, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata.

An dai dauke Shugaba Assimi da gaggawa, ko da yake babu tabbacin ko an ji masa rauni ko a’a, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) ya rawaito.

Sai dai daga bisani wani jami’in gwamnati ya tabbatar wa da AFP cewa shugaban na nan cikin koshin lafiya.

Tuni dai Shugaban ya koma sansanin sojoji da ke Kati a wajen birnin Bamako inda aka kara tsaurara matakan tsaro, inji jami’in gwamnatin.

Ministan Harkokin Addini na Kasar, Mamadou Kone ya shaida wa AFP cewa maharin ya yi yunkurin hallaka Shugaban ne da wuka amma bai yi nasara ba.

Latus Toure, Daraktan masallacin ya ce maharin ya yi hakon samun shugaban ne amma sai ya sami wani daban.

Mai kimanin shekara 37, an rantsar da Assimi Goita ne a watan da ya gabata, duk kuwa da irin matsin lambar diflomasiyyar da kasar ke fuskanta sakamakon juyin mulkin da aka yi har sau biyu cikin watanni tara.

A watan Agustan bara, Kanal Assimi ya jagoranci hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita bayan shafe watanni ana zanga-zanga ka gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaron kasar.