✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zangar adawa da tsadar Burodi a Sudan

Masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Omar Bashir ya sauka daga mulki.

Dubban mutane a Sudan sun ci gaba da gudanar zanga-zangar nuna adawa da karin farashin kudin Burodi a kasar.

Zanga-zangar da aka faro ta tun daga ranar Laraba ta ci gaba har zuwa Lahadi, inda jami’an tsaro a kasar suka harba barkonon tsohuwa tare da kame masu zanga-zangar da suka fito a sassa daban-daban na kasar.

Tsadar kayan masarufi a kasar ciki har da karin farashin Burodin ya tunzura dubban mutane shiga zanga-zangar, dadin-dadawa kasar na fuskantar karancin man fetur wanda hakan ya sa masu zanga-zangar ke bukatar shugaba Omar Bashir ya sauka daga shugabancin kasar.

Masuzanga-zangar sun kona tayoyi a kan manyan titunan kasar, yayin da wasu suka yi kokarin farmakar gidan gwamnatin kasar amma jami’an tsaro suka tari hanzarinsu.

Mutanen sun dage kan lallai sai shugaba Omar Bashir wanda ya dare karagar mulki tun 1989 ya sauka, sakamakon karancin abinci da koma bayan tattalin arziki da kasar ke fuskanta.