✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Liz Truss a matsayin sabuwar Firaministar Birtaniya

Ita ce za ta maye gurbin Boris Johnson

Jam’iyyar Conservative ta masu ra’ayin rikau a Birtaniya a ranar Litinin ta zabi Liz Truss a matsayin sabuwar Firaministan kasar.

Lis, wacce ita ce mace ta uku da ta dare kujerar dai za ta maye gurbin Boris Johnson ne, a daidai lokacin da kasar ke fama da rikicin tattalin arziki mafi muni a tsawon shekaru masu yawa.

Sabuwar Firaministar dai ita ce tsohuwar Sakatariyar Harkokin Waje ta Birtaniya, kuma ta doke abokin karawarta, kuma tsohon Ministan Kudin kasar, Rishi Sunak.

Ta sami kaso 57 cikin 100, yayin da shi kuma ya sami kaso 43 na kuri’un da mambobin jam’iyyar suka kada.

A wani gajeren jawabi ta bidiyo da ta wallafa bayan samun nasararta a wani dakin taro da ke tsakiyar birnin Landan, Liz Truss ta ce babbar girmamawa ce a gareta samun matsayin da ta jima tana hankoron samu.