✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Mohamed Salah gwarzon kwallon kafa na 2022

Dan wasan, wanda ya ci kwallo 30 a kakar wasa ta bana

Kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasar Ingila, ta zabi Mohammed Salah na kungiyar Liverpool a matsayin gwarzon dan kwallon kafa na 2022.

Kazalika, kungiyar ta kuma zabi Sam Kerr ta kungiyar Chelsea a matsayin gwarzuwar shekara a fannin mata.

Salah ya samu darewa wannan matsayi ne bayan da ya samu kashi 48 cikin 100 na adadin kuri’un da aka kada wanda hakan ya ba shi damar shigewa gaban dan wasan Manchester, City Kevin De Bruyne da kuma Declan Rice  na West Ham.

Dan wasan, wanda ya ci kwallo 30 a kakar wasa ta bana inda ya kara tagomashi ga yunkurin da Liverpool ke yi na daukar kofuna hudu, yana tattaunawa kan sabon kwantaragi inda kungiyar ke  fatan dan wasan zai ci gaba da zama a Anfield.

Wannan shi ne karo na biyu da Salah, dan shekara 29 daga Masar, ke lashe kyautar marubuta labaran kwallon kafa a Ingila.

’Yan wasan kungiyoyin biyu da suka fafata a gasar Premier, Liverpool da Manchester City ne suka mamaye kuri’un, inda kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya gabatar da ‘yan wasan su tara da ‘yan City shida.

Kerr, wanda kwallaye 18 da ya ci suka taimaka wajen daga kungiyar kwallon mata na Chelsea a gasar, ya samu kashi 40 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da ‘yar wasan gaban Arsenal ‘yar asalin kasar Holland, Vivianne Miedema ta zo ta biyu sannan Lauren Hemp ta Manchester City a matsayi ta uku.

Salah da Kerr za su karbi kyautarsu ne a wajen liyafar gwarzon kwallon kafa da za a gudanar ran 5 ga Mayu a London.

Shugabar FWA, Carrie Brown, ta ce, “Mo da Sam sun yi fice a kakar wasa ta bana, inda suka sauya tarihin kulob dinsu da na kasa.

“Kazalika kwazon da suke nunawa a filin wasa, ya tabbatar da su biyun gwaraza ne,” inji Carrie Brown.