✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi shugaba guda biyu a Majalisar Edo

Rikicin Majalisar Dokokin Jihar Edo ya kara kamari bayan rantsar da sabbin ‘ya’yanta 14 da aka ki rantsarwa watannin 13 da suka wuce. An rantsar…

Rikicin Majalisar Dokokin Jihar Edo ya kara kamari bayan rantsar da sabbin ‘ya’yanta 14 da aka ki rantsarwa watannin 13 da suka wuce.

An rantsar da ‘yan majalisar ne duk da cewar an tunbuke rufin ginin majalisar domin yin gyara, aka kuma zabi sabon Kakakinta.

Rikicin ya dauki sabon salo ne bayan tsige Mataimakin Kakakinta Yekini Idiaye, mai goyon bayan dan takarar gwwamnan jam’iyyar APC Osagie Ize-Iyamu.

Hakan na faruwa ne ‘yan makonni kafin zaben gwamnan na ranar 18 ga Satumba, 2020.

Sabbin ‘yan majalisar 14 sun yi wata 13 suna jira tsammani bayan rantsar takwarorinsu 10 masu goyon bayan Gwamna Godwin Obaseki.

— Sabbin ‘yan majalisa sun tsige kakaki

Wata majiya ta ce, sabbin ‘yan majalisar da wasu 2 ne suka tsige Frank Okiye suka kuma rantsar Victor Edoror a matsayin sabon Kakaki.

Majalisar ta fara shiga rikici ne a 2019, lokacin da a aka rantsar da ‘ya’yanta 10 kadai da ke goyon bayan Gwaman Obaseki.

Yanzu 17 daga cikinsu ne ke goyon bayan tsohon shugaban jam’iyyar APC, Kwamaret Adams Oshiomhole, 7 kuma na tare da Godwin Obaseki, dan takarar jam’iyyar PDP.

Wata majiya ta ce, tsohon magatardar majalisar, Tom Efezokhae, ya rantsar da ‘yan majalissar 14.

An kuma rantsar da Edoror, bayan ‘yan majalisar 17 sun amince da kudirin tsige tsohon kakakin majalissar.

Da aka nemi jin ta bakin sabon Magatakardan Majalisar, Yaya Omogbai sai ya ce, “Ba ni zan yi magana ba, ku tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a”.

Sai dai kuma Kakakin Majalisar da aka tsige, ya ce abun da ‘yan majalisar 14 suka yi cin zarafin kasa ne kuma sun yi zaben ne a gidan dayansu.


“Iya sani na mu goma ne a Majalisar Jihar Edo, sauran zababbun ‘yan majalisar 14 har yanzu suna kotu.

“Ni ne Kakakin Majalisar Jihar Edo”, inji Okiye a hirarsa da gidan talbijin na Channels.

Sabon Kakakin Majalisar, ya ce an riga an zabe shi, kuma duk abun da Majalisar ta yi karkashin jagorancin Okiye haramtacce ne.

Tun ranar Alhamis ‘yan sanda suka mamaye majalissar, yunkuri da shugaban jami’an tsaron da ke kula da majalisar ya ce ba daidai ba ne.

Shi ma Gwamna Obaseki, ta bakin mataimakinsa, Philip Shaibu, ya ce zai yi iya kokarinsa ya kare martabar majalisar.

—Rufe majalisar tamkar juyin mulki ne

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ‘yan sanda da aka girke a farfajiyar majalisar tamkar juyin mulki ne da danniya.

Kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya yi kira ga Sufeto Janar na ‘Yan sanda da ya gaggauta janye jami’ansa da ya tura ba bisa ka’ida ba.

— ‘Kulle majalisar barazana ce ga tsarin mulkin kasa’

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce mamaye Majalisar da jami’an tsaron suka yi tamkar ce ga tsarin mulkin kasa.

Atiku ya bayyana a shafinsa na Twitter, cewar idan ba tsarin doka, to babu batun a bi doka.

“Ya kamata a bar mutanen Edo su zabi wanda suke so ya mulke su. Kuma zabin nasu zai zo ne a 19 ga watan Satumba 2020”, inji shi.