✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An zargi fasto da damfarar mabiyarsa N55m

Kotu ta ba da umarnin tsare wani fasto a gidan gyara hali kan zargin sa da damfari wata mambar majami’arsa har Naira miliyan 55.

Kotun Lardi ta Daya da ke Birnin Tarayya Abuja, ta ba da umarnin tsare wani fasto a gidan gyara hali kan zargin sa da damfarar wata mambar majami’arsa har Naira miliyan 55.

Jami’i mai shigar da kara, Barista C.S Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin, mai suna Shariff Abudu, mai shekara 55, wanda limami ne a cocin Hope Resurrection and Glory Church da ke yankin Dawaki Abuja, ya aikaita hakan ne bayan sihirce mai karar mai suna Winifred Nambative mazauniyar yankin Gwarimpa, Abuja.

Ya ci gaba da cewa: “Ka ba ta kwayar barkono uku ka bukaci ta taunam sai ruwan roba don wanke fuskarta da kuma gabanta.
“Bayan nan ka karbi kudi daga wajenta da suka kai Naira miliyan 55 da dubu 45.

“Ka kuma bukaci ta gabatar maka da kwamfutocin hannu guda 6 da na’urorin kida na coci da kujeri da rigunan kaftani 20 da takalma 20 da rukunin jakunkuna, sai kuma biya maka kudin masauki a otel din Transcorp na Abuja jumla, ya kama Naira miliyan 50 da dubu 645.

“Ka aikata haka ne kan ikirarin umarni da ka ce ka samu a kanta daga wajen Ubangiji kan bukatar yi mata magani.

“Bayan ta koma hayyacinta ta bukaci ka mayar mata da kudin amma sai ka yi mata barazana tare da toshe layin wayarta daga wayarka.

“Saboda haka ana zargin ka da aikata laifuffukan zamba da da tursasawa, wadanda suka saba wa sassa na 325 da 397 a kundin dokokin manyan laifuffuka na Final Kod.”

Da aka waiwayi, wanda ake jarar ya musanta zargin tare da bukatar beli.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Sulayman Ola, ya ba da umarni a tsare shi tare da dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 28 ga Nuwamba.

Kotun ta ce za ta yi nazari tare da gindaya sharudan beli a nan gaba.