✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana addu’o’i da azumin rokon ruwa a Taraba

An fi wata daya rabon da a yi ruwan sama a wasu sassan Jihar.

Al’ummar Musulmi da Kirista sun fara addu’o’i da azumin kwana uku domin rokon Allah Ya saukar da ruwan sama a Jihar Taraba.

Al’ummomi manoma na gudanar da addu’o’i da azumin ne bayan daukewar ruwan sama na fiye da wata guda, wanda ya kawo bushewar amfani a gonaki.

“Aikata sabo ya yi yawa, kama daga kashe mutane barkatai, garkuwa da mutane da sauran munanan halaye da za su sa Allah Ya yi fushi da mu,” inji wani manomi, Nuhu Barau.

Nuhu ya ce bara warhaka yabanya ta yi kyau har manoma sun fara girbe wake ’yar wuri, ana shirin girbin masara ’yar wuri.

Shi kuma Yunana David, wanda shi ma manomin ne, ya ce babu abin da ya shuka a daminar bana saboda karancin ruwan sama, yana mai cewa ya zama wajibi a koma ga Allah a nemi gafara.

Yankunan da daukewar ruwan saman ta fi kamari a Jihar Taraba a bana su ne Kananan Hukumomin Bali, Ardo-Kola, Gassol, Ibbi da Karim Lamido.

Dubun dubatar mutane ne, ciki har da mata da kananan yara, suka yi tururuwa zuwa masallatai da coci-coci domin gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama, a yankin Maihula, Karamar Hukumar Bali.

Wakilinmu ya ce hakan abin ya kasance a kananan Karim-Lamido da Ardo-Kola da Ibbi.