✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana amfani da wuraren ibada wajen satar danyen mai —NNPC

An gano haramtattun rumbunan adana danyen man 344 a yankin Neja Delta.

Shugaban Kamfanin man Najeriya na NNPC, Mele Kyari ya zargi wasu wuraren ibada a kasar da karkata bututun man sa zuwa coci da masalatai domin satar man da ake turawa ta karkashin kasa.

Kyari ya bayyana hakan ne wajen ganawar da shugabannin hukumomin gwamnati ke yi da manema labarai ranar Talatar nan a Fadar Shugaban Kasa.

Ya ce wannan na daga cikin dalilan da kamfanin ya dakatar da tura mai ta cikin bututun zuwa sassan kasar.

Shugaban Kamfanin ya ce jami’an tsaron kasar sun gano akalla wurare 295 da aka fasa bututun don satar man a cikin tafiyar kilomita 200.

A cewar Mele Kyari, an kama mutane 122 da hannu a satar man tsakanin watan Afrilun bana da wannan watan na Agusta da ake ciki kadai.

Shugaban Kamfanin na NNPC ya ce haka ma jami’an tsaron sun gano haramtattun rumbunan adana danyen man 344 da tukwanen tafasa shi 355 da tankuna 759 da manyan motoci 37 da kuma jiragen ruwa 450 da barayin man ke amfani da su wajen safarar man a yankin Neja Delta.

Kamfanin man ya dade ya na zargin bata gari da fasa masa bututu su na satar man a jihohi da dama, matsalar da ta taimaka gaya wajen rage yawan man da ya ke fitarwa.

A makwannin da suka gabata, kamfanin ya sanar da cewar ya na asarar da ta kai gangar mai dubu 400 kowacce rana saboda satar man da barayi ke yi ta hanyar fasa bututu, kuma wannan matsala ta sa Najeriya ba ta iya fitar da gangar mai miliyan guda da dubu 800 da ake bukata kowacce rana domin kai wa kasuwannin duniya.

A taron da ta gudanar a farkon wannan wata, kungiyar OPEC ta koka akan yadda Najeriya ba ta iya samar da makamashin da ake bukata domin sayarwa kasashen duniya.

Sai dai shugaban NNPC ya ce daga shekara mai zuwa Najeriya za ta daina shigar da tacaccen mai cikin kasar muddin matatar man Dangote ta fara aiki, domin taimakawa matatun man sa wadanda ake aikin farfado da su.