✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana barazana ga rayuwata – Mawallafin Daily Nigerian, Jaafar Jaafar

Wata majiya ta ce wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun jima suna bin sahunsa tsawon lokaci.

Mawallafin jaridar nan ta intanet mai suna Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya yi gudu daga gidansa bayan ya yi ikirarin ana yi masa barazana ga rayuwarsa a ’yan kwanakin nan.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun jima suna bin sahunsa tsawon lokaci.

“Rayuwar Jaafar na cikin hatsari bayan wasu mutane da muke kyautata zaton ’yan ta’adda ne sun jima suna fakonsa a gidajensa na Abuja da Kano,” inji wani makusancinsa da bai so a bayyana sunansa.

A watan Oktoban 2018 ne dai dan jaridar ya wallafa wasu hotunan bidiyo inda a cikinsu aka ga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana karbar Dalolin Amurka da ake kyautata zaton na cin hanci ne daga wasu ’yan kwangiloli.

To sai dai a cikin wata tattaunawa da Sashen Hausa na BBC a watan da ya gabata, an jiyo Gwamna Ganduje na barazanar cewa suna nan suna shirin maganin wadanda suka fitar da faya-fayan bidiyon.

Hakan dai ya sa Jaafar din ya aike da wata wasika ga Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya yana cewa muddin wani abu ya same shi to Gandujen ne.

Rahotanni sun nuna cewa ko kafin buyan na Jaafar, sai da Sashen Sa’ido na Babban Sufeton ’Yan Sanda ya gayyace shi domin ya kare kansa daga wasu zargen-zargen tayar da zaune tsaye da kuma yunkurin bata sunan Babban Sufeton.