✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana bikin zagayowar ranar kafa kasar Saudiyya

Wannan shi ne karo na biyi da ake gudanar da wannan biki

A wannan Larabar Saudiyya ke bikin ranar da aka kafa kasar kusan shekara 300 da suka gabata.

Tarihi ya nuna karni ukun da suka shude, a shekarar 1727, lokacin mulkin marigayi Imam Muhammad bin Saud, ne ya hade yankunan da suka zama kasa Saudiyya a halin yanzu.

Wannan shi ne karo na biyu da ake bikin a ranar 22 ga watan Fabariru, wanda kuma aka fara gudanar da shi a bara.

Adel Abdulrahman al-Assoumi ya bayyana ranar a matsayin “ranar mubaya’a da biyayya ga wanda ya kafa kasar da kuma murna da nasarorin da ya samu a halin rayuwarsa.”

Gwamnatin kasar kan ba wa ma’aikata hutu albarkacin bikin wannan rana.

Shugabannin duniya na ci gaba da aika sakonnin fatan alheri ga Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Salman, saboda zagayowar ranar.

Shugaban Majalisar Saudiyya, Adel Abdulrahman al-Assoumi da sarkin Baharain, Hamad bin Isa Al Khalifa da  Shugaba Emomali Rahmon na Jamhuriyar Tajikistan da sauransu, na daga cikin wadanda suka aike da sakon fatan alheri ga Sarkin Saudiyya.