✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana bincike kan aman jini bayan karbar allurar COVID-19 a Kaduna

Sanarwar ta fito ne daga shafin Kwamishiniyar Lafiyar jihar.

Gwamnatin Kaduna ta ce ta fara bincike kan matar da aka gani cikin wani bidiyo tana aman jini bayan an yi mata allurar rigakafin COVID-19.

Sannan gwamnatin ta Kaduna ta yi alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Aminiya ta rawaito, wata mata wadda bidiyonta ya karade kafafen sada zumunta tana aman jini bayan karbar rigakafin COVID-19, a Sakatariyar Kaduna.

Kwamishiniyar Lafiya ta Jihar, Dokta Amina Mohammed Boloni, ta  sanar a ranar Alhamis cewa, cewarta, mutum 72,000 ne a jihar suka karbi rigakafin allurar, sai dai an samu mutum uku da suka shiga wani yanayi a sakamakon allurar.

“An yi wa mutum 72,000 rigakafin, kuma an samu mutum uku da suka shiga damuwa sosai a dalilin allurar. Da zarar an kammala bincike kan lamarin matar za a bayyana wa jama’a,” a cewar Boloni.