✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana bincike kan wanda ya yi lalata da gawa 99 a asibiti

Ya ajiye miliyoyin hotuna da bidiyo na laifuffukan da ya aikata a dakunan ajiye gawarwaki.

Jami’an tsaron da suke bincike a gidan wani ma’aikacin sashin lantarki na wani asibiti, mai shekara 67 kan zarginsa da kisan mata biyu, sun iske na’urar adana bayanai da ake amfani da ita a kwamfuta da faifan CD wadanda suke dauke bayanan yin lalatar da ya aikata.

Kafar labarai ta Sky News ta ruwaito cewa mutumin mai suna David Fuller, wanda ya amsa laifin kisan gillar da aka yi wa matan, Wendy Knell da Caroline Pierce a 1987 a ranar Alhamis, ya amince da yin lalata da gawarwakin mata da yara a tsawon shekara 12,kamar yadda kafar labarai ta BBC ta ruwaito.

Fiye da hotuna miliyan 14 da jami’an tsaro suka gano sun nuna abubuwan ban tsoro da yawa, ciki har da batsa da yara a faifan bidiyo da ke nuna Fuller yana lalata da gawarwaki a asibitocin garin Kent da ke Birtaniya.

An dai samu bayanan sirrin da ya boye a dakinsa, kuma sun yi cikakken bayani game da shekarun wadanda ya yi lalata da su a tsakanin shekarun 2008 da 2020, kamar yadda Sky News ta ruwaito.

Sakataren Lafiya na Birtaniya ya kaddamar da kwamitin bincike mai zaman kansa a kan David Fuller wanda ya dauki hoton kansa yana lalata da akalla gawarwaki 100 a wasu wuraren ajiye gawarwaki biyu na asibitin Kent sama da shekara 12 da suka gabata.

Hakan ya biyo bayan binciken Dabid wanda ya fito daga Heathfield da ke Gabashin Sussex, wanda ya amince cewa shi ne ya kashe Wendy Knell da Caroline Pierce a 1987.

Sajid Javid ya shaida wa Majalisar Dokokin Kasar cewa, binciken zai duba laifuffukan da “illar da hakan ya janyo wa kasa”.

Javid ya ce: “Zai taimaka mana mu fahimci yadda wadannan laifuffukan da suka faru ba tare da sanin mahukuntan asibitin ba, tare da tantance wuraren da ya kamata a ce an dauki mataki cikin gaggawa, sannan zai yi nazari a kan wasu manyan batutuwa da suka shafi tsarin kiwon lafiyar kasar ciki har da Hukumar Lafiya ta Kasa (NHS).”

Ya ce za a sake duba hukuncin da ake da shi a kan munanan laifuffukan da suka shafi lalata, bayan shari’ar don tabbatar da cewa, ‘sun dace’.

Mista Jabid ya kara da cewa, “Ina neman afuwar abokai da iyalan dukkan wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a karkashin kulawar Hukumar NHS.”

Fuller ya ajiye miliyoyin hotuna da bidiyo na laifuffukan da ya aikata a dakunan ajiye gawarwaki.

Ya dauki hotunan ne tsakanin shekarar 2008 da Nuwamban 2020, kuma ya sanya sunayen wadanda ya yi lalata da su a faya-fayen.

Fuller ya yi aiki a asibitoci daban-daban tun daga 1989 kuma ya yi aiki a asibitin Kent da Sussex har sai da aka rufe shi a watan Satumba 2011.