✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana bincike kan yadda aka zane wasu ’yan mata da bulala a Bauchi

Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi, ta tsunduma cikin binciken wani hoton bidiyo da a yanzu ya karade zaurukan sada zumunta wanda ya nuna yadda…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi, ta tsunduma cikin binciken wani hoton bidiyo da a yanzu ya karade zaurukan sada zumunta wanda ya nuna yadda wasu samari suna azabtar da wasu ’yan mata a Jihar.

A kallon tsanaki da wakilinmu ya yi, bidiyon ya nuna yadda wasu gungun samari suka tsare wasu ’yan mata kimanin su goma a cikin wani kango suna zane musu jiki da bulala daya bayan daya a birnin na Yakubu.

Jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Ahmed Muhammad Wakili cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Litinin a Bauchi, ya ce, “mun ankara da wani hoton bidiyo mai hade da sautin murya wanda ya nuna yada wasu gungun samari suna azabtar da wasu ’yan mata.”

DSP Wakili ya yi bayanin cewa, “bidiyon ya nuna yadda gungun wasu samari suka tirke matan kimanin su goma a wani kango suna cin zalinsu ta hanyar duka da bulalai.”

“Doriya a kan hakan samarin sun kuma rika yankar gashin ’yan matan da reza sannan suna ci musu mutunci da zage-zage don kara tsananta musu.”

Sanarwar da DSP Wakili ya fitar ta jajanta wa wadanda lamarin ya ritsa da su, ta kuma ce tuni an gayyaci ’yan matan domin su bayar da cikakken bayani da zai agaza wa jami’an ’yan sanda wajen gano wadanda suka aikata wannan lamari domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Kazalika, ya ce wannan azaba da aka yi wa ’yan matan abu ne mai firgitaswa wanda laifi ne daga cikin rukunin laifuka na cin zarafin jinsi.

“Jami’anmu sun dukufa wajen gudanar da bincike mai zurfi domin ganin an cafke tare da gurfanar da gungun masu hannu a wannan aika-aika a gaban Kuliya.”

“Kowace mace tana da ’yancin ta yi rayuwa ba tare da wani razani ba, tilastawa, cin zarafi, ko nuna mata wariya ba, kuma za mu dukufa wajen ganin cewa rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi za ta tabbatar musu da wannan ’yanci kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.