✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana binciken hadimin Ganduje kan kwace kudaden alarammomi

Ana zargin sa da sa matasa su kwace kashi 90 na kudaden da aka raba wa alarammomi

Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta Jihar Kano na bincike kan ruf da cikin kudade da ake wa mai taimaka wa gwamnan jihar, Ali Baba Agama-Lafiya.

Ana zargin sa ne da tura wasu matasa karkashin jagorancin dansa su karbe N45,000 daga cikin N50,000 da aka raba wa wasu alarammomin da suka yi wa jihar addu’o’i kan matsalolin tsaro da na annobar COVID-19.

Rahotanni sun nuna an ba wa alarammomin kudin ne domin su sayi ragunan layya da Babbar Sallah.

Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya shaida wa Aminiya cewa sun riga sun aike wa Ali Baba gayyata ya domin amsa tambayoyi.

“Muna da masaniya a kan zarge-zargen kuma tuni na umarci a fara bincike a kai.

“A ka’ida karbar kudaden daga hannun alarammomin ya saba da sassa na 22 da na 23 da suka kafa hukumarmu”, inji Muhuyi.

Ya ce sun samu tabbaci daga gwamnatin cewa an fidda kudaden kafin daga bisani a zargi dan Ali Baban da jagorantar wasu matasan wajen karbe N45,000 daga kowane alaramma bisa umarnin mahaifin nasa.

Ya ce daga bayanan da hukumarsa ta tattara ya zuwa yanzu, an tare malaman ne a kofar shiga gidan gwamnatin Kano inda a nan ne aka karbe musu kudaden.

“Idan zargin tabbataga to hakika raini ne ga gwamnan wanda shi ne ya ba su kudaden”, inji Muhuyi.

Shi ma a nasa bangaren, Kwamishina Harkokin Addini a jihar, Dakta Muhammad Tahar Adam ya tabbatar da samun korafin ko da dai ya ce Ali Baban yana karkashin ofishin gwamna ne ba ma’aikatarsa ba.

“Gwamna ya gayyaci alarammomi 360 domin su yi wa jihar addu’a kuma kowannensu an ba shi kasonsa a cikin takarda.

“Mun samu korafin karbar kudaden daga hannunsu amma gwamna ne kadai yake da hurumin daukar mataki a kai. Idan har hakan ta tabbata, to hakika ya aikata ba daidai ba”, inji kwamishinan.

Wasu majiyoyi da ke da kusanci da gwamnan sun shaida wa Aminiya cewa matakin da hukumar ya ki da cin hancin ta dauka shi ne matsayin gwamnan a kan batun.

Yunkurin Aminiya na jin ta bakin Agama-Lafiya ya ci tura saboda wayarsa ta kasance a kashe har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

To sai dai an ji shi a wata kafar yada labarai yana cewa shi ne ya umarci a karbi kudaden, kuma ya yi haka ne da nufin fadada wadanda za su ci gajiya daga cikin alarammomin, ba wai a aljihunsa zai zuba ba.

“Shawara na ba su na ce me zai hana maimakon kawai su karbi kudi su tafi a fadada abin ta yadda wasu karin alarammomin za su amfana.

“So muke a ce akalla alarammomi biyu da suke tare da gwamnan suma su ci gajiya”, inji wanda ake zargin.

Daya daga cikin alarammomin dan kimanin shekaru 60 ya shaida wa kafar yada labaran cewa bai taba mallakar N50,000 ba a rayuwarsa duk kuwa da cewa yana sana’ar dako a kasuwar Singa sai wannan karon kafin daga baya kuma a zo a yi musu yankan kauna.

Ya ce ya yi matukar takaicin yadda suka bige da kaso 10 kacal na adadin da aka ba su.

Bayan ya yi korafin wasu wasu matasa su uku suka zo suna ikirarin cewa su ‘ya’yansa ne suna so ya janye maganar don kada ya saka kansa a matsala, ko da yake ya ce ba su karyata batun karbe kudin ba.