✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana binciken kisan ma’aurata da jaririyarsu ’yar wata 8 a California

Jami’an tsaro a birnin California da ke Amurka, na binciken kan kisan wasu ma’aurata da jaririyarsu ‘yan watanni takwas. CNN ta ruwaito cewa, an tsinto…

Jami’an tsaro a birnin California da ke Amurka, na binciken kan kisan wasu ma’aurata da jaririyarsu ‘yan watanni takwas.

CNN ta ruwaito cewa, an tsinto gawarwakin mamatan ne a ranar Laraba a wata gona, bayan wani mutum dauke da makami ya yi garkuwa da su a farkon makon nan.

Wani manomi da ya gano gawarwakin, ya ce a wani lambu da ke gundumar Merced ya gano su, inda aka kwantar da gawar jaririyar a kusa da ta iyayenta, Jasleen Kaur da Jasdeep Singh.

Haka kuma, ya ce baya ga su akwai wata gawar ta Kawun jaririyar a kusa da su, wanda ganin haka ne ya sanya take ya sanar da mahukunta.

A wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba bayan gano gawarwakin, babban jmi’in dan sanda mai kula da yankin, Vern Warnke ya ce har yanzu ba su gano dalili kisan ba.

Sai dai ya ce sun kama wani mutum mai shekaru 48 da suke zargi, amma har zuwa ranar Laraba ba a kai shi kotu ba tukun.