✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An damke shugabar coci ‘yar damfara

Wata Shugabar cocin CCC da ke yankin Obada a Jihar Ogun ta shiga komar ’yan sanda bisa zargin ta da damfarar wasu mutane kudi sama…

Wata Shugabar cocin CCC da ke yankin Obada a Jihar Ogun ta shiga komar yan sanda bisa zargin ta da damfarar wasu mutane kudi sama da Naira miliyan biyu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta ce ta dade tana neman wacce ake zargin, Oluwakemi Sotonode sakamakon korafin da wani mutum mai suna Idris Iliyas ya shigar a kanta.

“An yi nasarar kame ta a ranar 6 ga watan Oktoba inda ta amsa laifinta za kuma a gurfanar da ita a kotu da zarar an kammala bincike”, inji Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi.

Ya bayyana cewa a watan Nuwanban 2019 ne Iliyas ya kai wa rundunar kara cewa matar ta umarce shi ya kai wa wani kamfani dutsen Kaolin na Naira 2,200,000, amma ta zagaye ta karbe kudin ta yi sabgar gabanta.

Kazalika a watan Satumbar 2020, wacce ake zargin ta karbi Naira 200,000 a wurin wani mai suna Olabangboye Olalekan cewa za ta sayar masa da fili a yankin Obada-Oko amma ta yi tsere da kudin.

Gabanin haka, a watan Afrilu ta karbi Naira 300,000 2020 daga wani kamfani bayan ta sa wani mai suna Kehinde Ojekunle ya kai wa kamfanin dutsen Kaolin, inda nan ma ta zagaye ta karbe kudin.

DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce, ya kara da cewa a watan Maris ma matar ta karbi Naira 670,000 daga hannun wata mace mai suna Gbolagade Damilola cewa za ta sayar mata da shinkafa buhu 40, amma ta tsere da kudin.

“Wadannan tuhume-tuhume da ke kan shugabar cocin ne suka sa Kwamishina ’Yan Sandan Jihar Ogun, Edward Ajogun, ya umarci a kama ta”, inji DSP Oyeyemi.