✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana jiran sakamakon zaben Shugaban Kasar Nijar

Mutum 30 na takarar Shugaban Kasa, 5,000 kuma na fafatawa a zaben Majalisar Dokoki.

A halin yanzu ana dakon sakamakon zaben Shugaban Kasar Nijar wanda aka gudanar a ranar Lahadi.

Zaben wanda ’yan takara 30 suke fafatawa a ciki shi ne na farko da bayansa zababben Shugaban Kasar zai mika wa na bayansa mulki.

An yi zaben ne tare da na ’yan Majalisar Dokokin Kasar mai kujera 171 wanda mutum 5,000 ke takara a cikinsa.

Da almurun ranar Lahadi ce aka rufe rumfunan zaben da Hukumar Zaben kasar ta ce akalla mutum miliyan bakwai ne a fadin kasar ke jefa kuri’a.

Zaben ya gudana ne a lokacin da ake fama da matsalar tattalin arziki a kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin mafi talauci a duniya; Bankin Duniya ya ce akalla 40% na ’yan  kasar matalauta ne.

Kasar na kuma fama da matsalar tsaro mai kaifi biyu: mayakan ISIS a yankin Sahel (Burkina Faso da Mali), da kuma Boko Haram (daga bagaren Najeriya).

Gabanin zaben dai wasu mayaka sun kashe sojoji bakwai da fararen hula ’yan Najeriya 34 a yankin Diffa na kasar.

Ko kafin nan, Boko Haram ta kashe mutum 50 daga Jihar Bornon Najeriya da ke gudun hijira a Nijar.

Rahotanni sun nuna jama’a musamman a yankin na Diffa na zaune cikin zullumi saboda karuwar ayyukan maharan.

Mai bincike da sharhi kan ta’addancin Boko Haram, Bulama Bukarta ya ce kungiyar ta gargadi mazauna su guji zuwa rumfunan zaben na ranar Lahadi.

Ya wallafa a shafinsa cewa al’ummomi yankunan sun roki jami’an da suka je yankunansu domin gudanar da zaben Shugaban Kasa su tattara kayansu su tafi.

A cewarsa, karar harbin bindiga a wasu sassa na yankin ya haifar da karancin fitowar mutane wajen zaben.

Babu dai wata majiya ko hukuma da ta tabbatar da ikirarin nasa kawo yanzu.