✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ana kokarin korar ma’aikatan lafiya 600 a Kaduna saboda shiga yajin aiki’

Ya ce a cikinsu har da wasu mutum biyu da ’yan bindiga suka sace makonni bakwai da suka gabata.

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma ta Kasa (NANNNM) reshen Jihar Kaduna ta ce Gwamnatin Jihar na barazanar sallamar mambobinta 600 daga bakin aiki saboda shiga yajin aiki.

Shugaban kungiyar a Jihar, Kwamared Ishaku Yakubu ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya a Kaduna ranar Laraba.

Ya ce tuni Gwamnatin Jihar ta kammala tattara sunayen ma’aikatan su 1,300, kafin daga bisani ta rage adadin zuwa 600.

Idan za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Mayun 2021 ne Gwamna Nasir El-rufai ya sanar da korar dukkan ma’akatan jinyar da ke kasa da matakin albashi na 14 a Jihar saboda shiga yajin aikin gargadin da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi.

Bugu da kari, Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da ta tallata gurabe domin dibar sabbin ma’aikatan da za su maye gurbin wadanda aka kora.

To sai dai Kwamared Ishaku ya ce da alama fa har yanzu Gwamnan na nan a kan bakarsa kan korar ma’aikatan da suka shiga yajin aikin.

A cewarsa, Gwamnatin ta cire sunayen wadanda ke hutunsuu na shekara, da wadanda suka tafi karo karatu ko haihuwa, amma ta hada har da wasu mutum biyu da ’yan bindiga suka sace makonni bakwai da suka gabata.

Shugaban kungiyar ya ce tuni suka sanar da uwar kungiyar tasu ta kasa a kan yunkurin Gwamnatin.

Sai dai kokarin Aminiya na jin ta bakin Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Aisha Baloni kan lamarin ya ci tura saboda ba ta amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike mata da shi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.