✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana neman mafarauta ruwa a jallo saboda kashe Dorinar Ruwa a Taraba

An haramta farautar Dorinar Ruwa a Jihar Taraba.

An bazama wajen neman wasu mafarauta 14 ruwa a jallo saboda kashe wata Dorinar Ruwa a Jihar Taraba.

Gwamnatin jihar ce ta ba da umarnin kamo mafarautan da suka fito daga garuruwan Mayorenewo, Binnari da Shagarda da ke kusa da Kogin Namnai wanda ya yi iyaka da Kananan Hukumomin Ardo-Kola, Karim-Lamido da Gassol.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana zargin mafarautan sun kashe Dorinar Ruwan ce a Kogin Kwoi kusa da kauyen Bajimba da ke Karamar Hukumar Gassol.

Bayanai sun ce mafarautan wanda suka kashe Dorinar Ruwan a makon jiya sun kuma yi kasafin namanta a tsakaninsu.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun gabanin yanzu Gwamnatin Jihar ta bayar da umarnin da yake haramci da farautar Dorinar Ruwa a duk fadin jihar.

Sai dai bincike ya gano cewa mafarautan da ake nema ruwa a jallo sun kamo Dorinar Ruwa a cikin sirri sannan suka harbe ta.

Bayan harbe Dorinar Ruwan ce suka kai ta cikin jeji nesa da kogin da suka kamo ta suka daddatsa namanta.

Rahoton kashe Dorinar Ruwan ya samo asali ne daga wata kungiyar mafarauta da ta kulla adawa da ta wadanda suka yi watandar Dorinar Ruwan ba tare da su ba.

Bullar wannan rahoton ne ya sanya gwamnatin jihar ta ba da umarnin kamo wadanda suka yi wa umarnin nata karan tsaye, inda wasunsu suka buya yayin da kuma wasu suka tsere suka bar iyalansu domin gudun shiga hannu.

Wani jagoran al’umma a garin Mutum Biyu, Mai shari’a Sani Muhammad (mai ritaya), ya shaida wa Aminiya cewa wannan abin takaici ne la’akari da yadda mafarautan suka yi wa umarnin gwamnatin kunnen uwar shegu duk da kashedin da ta yi.

Kwamishinan Muhalli na Jihar, Alhaji Ibrahim Lawal, ya shaida wa Aminiya cewa tuni bincike ya kankama a kan lamarin kuma yana da yakinin mafarautar da suka yi wannan aika-aika za su shiga hannu domin su girbi abin da suka aikata.