✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana safarar makaman yakin Rasha da Ukraine zuwa yankin Tafkin Chadi – Buhari

Ya ce lamarin na kawo kalubalen tsaro ga yankin

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa ana safarar wasu daga cikin makaman da ake fafata yaki tsakanin Rasha da Ukraine zuwa yankin Tafkin Chadi.

Buhari ya furta haka ne ranar Talata, lokacin da yake jawabi yayin bude taron Shugabannin Kasashen Hukumar Raya Tafkin Chadi (LCBC), karo na 16 a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Taron ya sami halartar dukkan shugabannin kasashe shida na yankin, in ban da Paul Biya na Kamaru, wanda daya daga cikin Ministocinsa ya wakilta.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Jamhuriyyar Afirka ya Tsakiya, Farfesa Faustine Archange Touadera da na Nijar, Mohamed Bazoum da na Benin, Patrice Tallon da Shugaban rikon kwarya na Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, da kuma Shugaban mulkin soja na Libya, Mohamed Al- Menfi.

Shugaba Buhari, wanda kuma shi ne shugaban taron, ya ce lamarin, wanda ya kara yaduwar kanana da matsakaitan makamai a yankin, abin damuwa ne.

Daga nan sai ya yi kira da kasashen yankin da su dada tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinsu domin magance kalubalen.

Buhari ya kuma ce shigowar makaman na yakin Rasha da Ukraine ya dada ta’azzara rikicin Boko Haram da na ta’addanci a yankin.

Sai dai ya ce duk da nasarorin da gwamnatinsa ta samu na kawo karshen Boko Haram da sauran ’yan ta’adda, har yanzu akwai ragowar barazanarsu.