✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana samun karuwar cin zarafin mata a gidajen nishadantarwa a Saudiyya

Mata da maza sun gwamutsa wuri guda, ana ta hada-hada fiye da tunanin dan Adam.

Bayan da aka gudanar da bikin kalankuwar mawaka mafi girma a yankin Gabas ta Tsakiya a kasar Saudiyya, wadanda suka shirya bikin sun yi alkawarin daukar matakan kare cin zarafin mata ta hanyar lalata da sauransu a inda aka gudanar da bikin a wajen birnin Riyadh.

A yanzu taruwar jama’a domin gudanar da wani abin nishadi ba bakon lamari ba ne a Saudiyya, sai dai ana samun rahotanni nan da can daga matan kasar da na kasashen waje, kan yadda ake ci zarafinsu, wasu daga ciki ma an dauka a bidiyo.

Har yanzu wadansu mutanen Saudiyya suna mamakin yadda kunnuwansu ke jiyo karar kadekade da raye-raye a kasar da a shekarun baya ba ka isa sanya kida ba, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kwana hudu mawakan MDLBeast’s Soundstorm suka kwashe suna cashewa kuma dubban ’yan kallo ne suka tiki rawa a wasan makadan da suke tashe a duniya.

Mata da maza sun gwamutsa wuri guda, ana ta hada-hada fiye da tunanin dan Adam.

Fitattun mawaka daga sassan duniya ne suka yi nazari kan zargin take hakkin dan Adam da ake yi a Saudiyya kafin yanke hukuncin halartar bikin, yayin da masu fafutuka suke cewa wadanda suka halarta sun ce sun yi ne domin wanke bakin fentin da gwamnatin kasar ta yi a idon duniya kan take hakkin dan Adam.

Sai dai ba su kadai ne suka sake tunani kafin yanke hukuncin zuwa ba, an samu rahotannin cin zarafin mata a wurare dabandaban musamman a kusa da wuraren da aka gudanar da bikin a Riyadh da wasu wurare.

Bidiyo da dama sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta a shekarun da suka gabata kan yadda maza suke cin zarafin mata.

MDLBeast sun kaddamar da gangami mai taken a mutunta a kuma dauki matakai domin bai wa mata kariya a irin wadannan wuraren, tare da daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga wadanda aka samu da laifin cin zarafin mata.

Tun shekarar 2018, hukumomin Saudiyya suka bayyana duk wani nau’in cin zarafi a matsayin babban laifi da ba za amince da shi ba, an kuma a je hukuncin dauri a gidan yari na shekara biyar da tara mai tsanani a kan wadanda suka aikata haka.

Sai dai yawancin matan Saudiyya da kafar labarai ta BBC ta tattauna dasu sun shaida mata cewa ba su yarda da matakin da hukumomin suka ce suna dauka ba.

Babu wata daga cikin matan da ta amince a ambaci sunanta. Sun ce kodai sun fuskanci cin zarafin ko kuma wata da suka sani an ci zarafinta a irin wadannan wuraren na bukukuwan nishadi.

Wata daga cikinsu ta ce an yi ta dora laifin yawancin hotuna da bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta a kan matan, sannan akwai yiwuwar a hukunta su a karkashin dokokin Saudiyya.

Wata daban kuma, ta ce hukumomin suna daukar mataki ne idan lamarin ya hada da ’yar kasar waje.

Ta kara da cewa ana yi wa batun rikon sakainar kashi idan lamarin ya hada da matan Saudiyya, sai dai ana daukar matakin mummunan hukunci da tara mai tsanani a kan matar.

Mace ta uku ta ce ba a bai wa mata wata kariya ta zahiri, lamarin da ya sa suke jin da ma ba su je ba, da ba su je din ba da hakan ba za ta faru ba.

Idan mace ta kai rahoton an ci zarafinta, tana fuskantar tsangwama ko ma Allah wadai daga ’yan uwa da sauran al’umma.

‘Sauyi a zahiri’

Makusantan Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman da a fakaice shi ke jagorantar kasar da kuma abokansa sun ce wadannan lamura na faruwa ne sakamakon yadda kasar ke kokarin sauya wasu dabi’u da al’adun da aka yi shekaru aru-aru ana bin tsarinsu, musamman wadanda masu ra’ayin addinin Musulunci suka shimfida.

Tsarin sauye-sauyen da kasar ke dauka na tafiya da sauri domin fatar ganin an cimma muradun Bision 2030 na sauya Saudiyyar ba ki dayanta, ta hanyar dauke hankali daga dogaro ga man fetur, tare da bai wa matasa damar a dama da su a fagagen rayuwa daban-daban.

Magoya bayan Yariman sun ce duk wadannan abubuwan suna faruwa ne a matakin farko, sun yi kiran a kara yin hakuri domin ana shirin daukar matakan da suka fi wadanda ake gani a yanzu.

Amma matan Saudiyya da suka tuntubi BBC, sun sa ayar tambaya a kan sahihancin haka, tare da nanata cewa matan sun dade suna fatar ganin ana tattauna matsalolinsu da magance su, amma babu abin da aka yi.

Sun ce batutuwan cin zarafi suna daga cikin abubuwan da suka tsaya a zukatan matan Saudiyya, kama daga halartar manyan tarurrukan da maza da mata za su cudanya da sauransu, wanda ana yi ne da nufin a bude kofar kasar ga sauran kasashe ba wai ta fannin yawon shakatawa