✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zanga-zanga kan sauya kundin tsarin mulki a Tunisiya

Daruruwan mutane na gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis na kasar Tunisiya, don nuna adawa da daftarin kundin tsarin mulkin da shugaba kasa Kais Saied…

Daruruwan mutane na gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis na kasar Tunisiya, don nuna adawa da daftarin kundin tsarin mulkin da shugaba kasa Kais Saied ya gabatar.

Masu boren da suka soma zanga-zangar a ranar Asabar, sun bukaci shugaban kasa ya yi murabus kwanaki biyu kafin a kada kuri’ar amincewa da kundin tsarin mulkin.

Bayanai sun ce kundin tsarin mulkin zai kunshi karin iko da Saied ya yi amfani da su tun bayan da ya kori gwamnati tare da dakatar da majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga watan Yulin bara.

Ana kallon matakin Shugaba Saied a matsayin wani babban komabaya ga tsarin siyasa mai cike da rikici a Tunisiya, kuma masu hamayya da shi na zargin kundin tsarin mulkinsa na da nufin maido da mulkin kama karya.

Za a gudanar da kuri’ar raba gardama ne shekara guda bayan da Saied ya kori gwamnati tare da dakatar da majalisar dokokin kasar a wani zagon-kasa da ke adawa da mulkin dimokuradiyyar matasa masu cike da rudani a kasar ta Tunisiya