✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin maganin tari ya kashe yara 66 a Gambiya —WHO

Magungunan su ne: Promethazine Oral Solution da Kofexmalin Baby Cough Syrup da Makoff Baby Cough Syrup da kuma Magrip N Cold Syrup

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara bincike kan maganin tari samfurin kasar Indiya da ya yi sanadiyar mutuwar yara 66 a kasar Gambiya.

A ranar Laraba WHO ta yi gargadi kan yin amfani da wasu magunguna sanyi da tari guda hudu da kamfanin Maiden Pharmaceuticals da ke Indiya ke sarrafawa.

Hukumar ta ce akwai yiwuwar matuwar yaran Gambiya din na da alaka da wadannan magungunan.

Ta kara da cewa, akwai kuma yiwuwar an tura gurbatattun magungunan zuwa wasu sassan Afrika baya ga yankin Afrika ta Yamma, da kuma zuwa sassan duniya.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ana zargin magungunan da ake batu suna yi wa koda illa da kuma kashe mutum 66 a tsakanin kananan yara a kasar.

“Mutuwar wadannan yara ba karamin tashin hankali ba ne ga ’yan uwansu,” in ji Ghebreyesus.

Magungunan da lamarin ya shafa su ne: Promethazine Oral Solution da Kofexmalin Baby Cough Syrup da Makoff Baby Cough Syrup da kuma Magrip N Cold Syrup.

Ko a watan da ya gabata, Ma’aikatar Lafiya ta Gambiya ta ba da sanarwar asibitocin kasar su daina amfani da wani maganin Farasitamol na ruwa har sai an kammala binciken mutuwar wasu yara akalla 28 wanda lalurar koda ta kashe a kasar.