✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin ’yan sanda da bindige matashi har lahira a Zariya

Matashin ya zo wucewa ne bai ji ba bai gani ba lamarin ya ritsa da shi

Ana zargin jami’an ’yan sanda da bindige wani matashi mai shekara 20 a duniya mai suna Yusuf Adamu da ke unguwar Dakace a Zariyan Jihar Kaduna, inda ya mutu nan take.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jami’ain ke kokarin tarwatsa wata zanga-zanga da matasa suka yi a garin na Dakace.

Zanga-zangar ta samo a asali ne sakamakon zargin harbin da wani dan sanda mai suna Yakubu Buba ya yi wa wani matashi mai suna Sama’ila Musa a lokacin da suka je wajen shaye-shayensu.

Aminiya ta ziyarci unguwar da lamarin ya faru, inda ta gano matashin da dan sanda Buba da ake zargi ya harba bai mutu ba, amma yana asibiti inda yake karbar magani

Sai dai al’ummar unguwar sun shiga cikin jimamin rashin matashi Yusuf da jami’an ’yan sanda suka harba a kai wadda ya yi sanadiyar rasa ransa.

Lamarin ya faru ne da yammacin Talata da ta gabata inda matasan anguwar  Dakace suka fito dan nuna rashin jin dadin su bisa yadda suke zargi an yi harbin.

Zaga-zagar matasan wadda ta kai da tsare hanyar Jos zuwa Zariya, ta kai har da fara kone-konan tayoyi dan nuna rashin jindadin su akan abinda ya faru.

Bayanai na nuni da cewa a kokarin tarwatsa masu tarzomar da ’yan sanda suka yi ne ya yi sanadiyar rasa ran matashi Yusuf Adamu, a kan hanyarsa ta komawa gida daga wurin sana’arsa ta aikin gyaran mota.

Maihaifin marigayin, Adamu mai anguwa, ya shaida wa Aminiya cewa, “Jami’an ’yan sanda ne suka harbe dana mai suna Yusuf Adamu a kai wadda ba cikin ’yan zaga-zagar ma yake ba.”

Mahaifin yaron ya Bukaci hukumomi da gwamnati da subi kadin kisan gillar da aka yi wa dansa ba tare da ya aikata laifin komai ba.

Sai dai da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce bai riga ya sami bayanin lamarin ba a hukumance, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin kuma, har yanzu bayanai na nuni da cewa ba a riga an yi jana’izar matashin ba, saboda wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam na kokarin gudanar da bincike da nufin kwato wa iyalan mamacin hakkinsa.