✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Anambra: Yayin da ake shirin bude rumfunan zabe

Ana fargabar masu zabe ba za su fito sosai ba saboda wasu dalilai

Nan da sa’o’i kadan ne ake sa ran bude rumfunan zabe a Anambra, inda masu kada kuri’a za su zabi gwamnan Jihar na gaba.

Ko da yake Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta kammala shiryawa don gudanar da zaben, an bayar da rahoton cin karo da matsaloli a wasu kanan hukumomin.

Mutum miliyan 2.5 ne dai ke da rajistar zabe, sai dai akwai fargabar jama’a ba za su fito sosai ba.

Duk da janye umarninta na zaman gida da kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra ta yi ranar Alhamis, wakilan jaridar Daily Trust sun bayar da rahoton yadda jama’a suka kasance cikin gida ranar Juma’a.

Wani mazaunin Awka, babban birnin Jihar, ya shaida wa Felix Onigbinde cewa, “Kamar yadda ka sani an yi ta samun tashin-tashina a Jihar Anambra, sannan kuma ga jibge dimbin jami’an tsaro da aka yi – mai yiwuwa wadannan dalilan ne suka hana mutane fitowa saboda suna tsoron abin da ka je ya zo”.

Kamar yadda masu iya magana kan ce, yaya lafiyar kura – da ma dai Jihar Anambra ta yi kaurin suna wajen rashin fitar masu zabe, balle kuma an samu matsaloli nan da can.

‘Laifin jami’an tsaro ne’

Wasu kunigyoyin farar hula na yankin Kudu maso Gabas ma dai sun yi zargin cewa dabi’un jami’an tsaron da aka kai sun taimaka wajen kara zaman dar-dar a jihar.

Kungiyoyin sun zargi jami’an tsaron da harbi kan mai uwa da wabi, da kama mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Sai dai kuma hukumomin tsaro sun karyata wadannan zarge-zarge, suna cewa manufar kai jami’an ita ce karfafa gwiwar masu zabe.

Ana saura kusan sa’a 24 a fara zaben ne dai aka sauya babban jami’in rundunar ’yan sanda mai kula da tsaro na musamman a Jihar, DIG Joseph Egbunike, aka maye gurbinsa da AIG Zaki Ahmed.

Wannan mataki dai ya jawo ce-ce-ku-ce, amma mai magana da yawun rundunar da ke kula da tsaro yayin zaben, DSP Nkeiruka Nwode, ta shaida wa wakilin Daily Trust Jude Aguguo Owuamanam cewa ba wata boyayyiyar manufa.

‘INEC ta shirya’

Hukumar INEC dai ta ce duk wani mataki da ya kamata a dauka don gudanar da zaben an dauka, kuma komai zai tafi yadda aka tsara duk da kalubalen da aka fuskanta.

Wakilin Daily Trust Abbas Jimoh ya ruwaito Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, yana fadar haka a wani sako da ya aike wa ma’aikatansa ranar Juma’a.

“Babu gudu ba ja da baya a kudurinmu na tabbatar da cewa an gudanar da wannan zabe kamar yadda aka tsara.

“Don haka ne muka gyara gine-ginenmu muka kuma sauya kayan aikinmu [wadanda aka lalata], sannan muka bukaci – muka kuma samu – tallafi da goyon baya daga jami’an tsaro, da jam’iyyun siyasa, da ’yan Takara da sauran masu ruwa da tsaki.

“Mun kuma aika da dukkan kayan zabe a kan lokaci, mun tura jami’an zabe, sannan mun tanadi dukkan abubuwan da ake bukata don kai kayan aiki da ma’aikata zuwa dubban wurare a Jihar Anambra…”, inji Farfesa Yakubu.

Kalubale a wasu wurare

Wakilan Daily Trust sun bayar da rahoton yadda ake ta kai-kawo a hedkwatar INEC da ke Awka ana ta hidimar shirya wa zaben.

Sai dai kuma akwai rahotannin samun kalubale a wasu kananan hukumomi, musamman ta fuskar kai jami’an zabe na wucin gadi wuraren da za su yi aiki.

Misali, masu sa ido a karkashin Shirin Bayar da Labarin Zabe na Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Premium Times sun ba da rahoton cewa har zuwa kusan karfe 9.30 na daren Juma’a, ma’aikatan wucin gadi sun yi cirko-cirko a hedkwatar INEC ta Karamar Hukumar Ogbaru, ba tare da an ma shaida musu lokacin da za su kama hanyar tafiya inda za su yi aikin ba.

Ko da yake an danka wa ko wanne jami’i kayan aikin da yake bukata a lokacin, babu ababen hawan da za su kai su cibiyoyin da ya kamata su je.

Yanzu dai kallo ya koma Anambra, inda miliyoyin ’yan Najeriya suka zuba ido su ga yadda za a gudanar da wannan zabe wanda wasu ke ganin zai zama zakaran gwajin dafi wajen gudanar da zabubbuka a kasar da ke kara fuskantar matsaloli daban-daban, musamman ta fuskar tsaro.