✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu’ sauran mai cutar coronavirus a Taraba

Mutumin da ya rage mai dauke da annobar coronavirus a jihar Taraba ya warke har an sallame shi. A ranar 20 ga wata ne Hukumar…

Mutumin da ya rage mai dauke da annobar coronavirus a jihar Taraba ya warke har an sallame shi.

A ranar 20 ga wata ne Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tabbatar da kamuwar mutumin da cutar.

A ranar Laraba 27 ga wata Kwamishinan Lafiyan Jihar, Innocent Vakkai ya tabbatar da sallamar mutumin bayan warkewarsa daga cutar.

Vakkai ya ce yanzu babu sauran wanda ke da cutar annobar coronavirus da ke addabar duniyar a fadin jihar Taraba.

Ya kara da cewa gwajin annobar cororavirus da aka yi wa mutum 15 da aka dauki jininsu ya nuna ba su harbu da cutar ba.

Vakkai shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da cutar coronavirus na jihar ta Taraba.